Gwamnatin Jonathan Tana Kara Jawowa Kanta Rigima

Shugaba Goodluck Jonathan

Gwamnatin Jonathan na cigaba da fadawa cikin rigingimu da ta haddasawa kanta sabili da wasu matakai da take dauka ba tare da la'akari da bin tafarkin dimokradiya ba, tana wasu abubuwa tamkar ana cikin mulkin soja.
Gwamnatin tana anfani da jami'an tsaro ta hanyar da bata dace ba lamarin dake kara haddasa mata rigingimu.

Jami'an tsaron sun fara hana 'yan jarida walwala da kwace masu kayan aiki ko kuma rufe masu ma'aikatarsu da ofisoshinsu har da ma rufe shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Har wayau gwamnatin tana yakar wadanda ke fafitikar a kubutar da 'yan matan Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram ke garkuwa dasu.

Bugu da kari gwamnatin ta shiga kafar wando daya da wasu gwamnoni ta kuma hana jiragensu sauka a birnin Kano domin hana manyan mutane dake zuwa taya sabon sarkin Kano murna sauka.

Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari dangane da irin wadannan rigingimu da gwamnatin tarayya ke haddasawa kanta ta takurawa mutane da kafofin labaru da yin mulki irin na soja cikin shirin dimokradiya. Gwamnan yace jayayya ita ce adon dimokradiya kuma gyara kayanka ba sauke mu raba ba ne. Shugabanni na ganin kamar suna da iko na wuka da nama a hannunsu wanda kuma a dimokradiya ba haka ba ne. Akwai abun da shugaba bashi da iko akai. Al'umma ke da cikakken iko. Idan ba al'umma babu shugaba.

Idan ba'a bi tsarin ba yadda yamakata za'a cigaba da samun rigingimu. Yin anfani da sojoji da 'yansanda domin gallazawa 'yan adawa misali gwamnan Rivers da abun da ya faru a Kano ba dimokradiya ba ne. Tamkar ana yiwa 'yan adawa isgilanci ne.

Saidai gwamnan Zamfara yace kowane lamari akwai matakin da yakamata a bi kuma zasu bi matakan da suka dace domin su tunkari isgilanci da ake yi masu. Kuskure ne shugaban kasa ke yi domin 'yansanda da sojoji ba nashi ba ne na kasa ne. Su sojojin da 'yansandan da suke ganin kamar suna yiwa shugan kasa aiki ne sun yi kuskure. Kasa yakamata su yiwa aiki.

Ga cikakken bayani daga Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jonathan Tana Kara Jawowa Kanta Rigima - 5'25"