Zaman sulhu da aka kuduri aniyar yi tsakanin mataimakin Gwamnan jihar Sokkoto Mukhtar Shehu Shagari, da mutumin da ya kada shi a zaben fidda dan takarar Gwamna Senata Abdullahi Wali, wanda yake tare da tsohon Gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, da uwargidan shugaban kasa za ta shiga tsakani, ya rikida ya zama gangamin yakin neman zabe na shugaban kasa.
Ministar kula da harkokin mata Hajiya Zainab Maina, wacce ta wakilci uwargidan shugaban kasan tace taje jihar ne domin ta karfafawa mata guiwa na jam'iyyar PDP ganin zabe ya kawo jiki.
Kan korafin da kungiyoyi da daidaikun mata suke yi cewa, ana ci da guminsu a fagen siyasa, inda sune suka fi kowa kada kuri'a, amma idan aka duba suna baya ta ko wani rukuni, Hajiya Zainab tace duk da haka, ita dai gwamnatin shugaba Jonathan ta taka rawar gani wajen tunkararar bukatun mata a fannin kiwon lafiya, da zaman takewa.
Hajiya Zainab tace gwamnatin tarayya tana tanade tanade dangane da bukatun mata musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, inda rikicin Boko Haram ya tagayyar da mutane masu yawa musamman mata, wadanda rikicin ya kashe mazajensu ya barsu da yara.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5