Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Jonathan Ya Ce Yana da Ikon Cire Kowa Daga Mukami


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Yayin da 'yan jarida suka yiwa shugaban kasa tambaya akan ko zai cire shugaban INEC sai yace yana da ikon cire kowa ya nada kan mukami

An tambayi shugaban kasa akan dage zabe ya musanta amma kuma ai sun dage zaben.

Yanzu ana rade- radin cewa tun da Farfasa Jega zai sauka a watan Yuni bisa ga doka zai tafi hutu watanni kafin cika lokacinsa. Sabili da haka gwamnati na neman yin anfani da wannan damar ta turashi zuwa hutu ta maye gurbinsa da dan amshin shatansu.

Ganin haka ana ta yin kururuwa a duniya ana ta yekuwa sai gwamnati ta karyata batun. To amma inji Dr Usman Muhammad a sa idanu aga abun da zai faru nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Akan abun da 'yan Najeriya zasu iya yi Dr Muhammad yace wajibi ne su tashi su kare hakinsu. Su dubi kasashen duniya da suka yiwa gwamnatocinsu ca domin sun zaluncesu. Mutane sun fita kan titi suka kalubali gwamnatocinsu da suka ci amanar kasashensu. Da ikonsu sai da suka canza gwamnatocinsu.

Yace a Najeriya an kusa kaiga hakan. Lokacin da aka cire tallafin man fetur ai 'yan Najeriya sun fantsama kan tituna sun ki amincewa da abun da gwamnati tayi. Yanzu ma sun samu daman fitowa su yaki gwamnatin. 'Yan Najeriya su fito ba tare da tashin hankali ba su nemi hakinsu.

Dr Usman Muhammad yace kada a kaucewa kundun tsarin mulki. A bi doka da oda. A kuma yi zabe lokacin da yamakata. Wajibi ne kowane dan Najeriya ya tabbatar an yi zabe domin hakinsa ne. Tilas shugaban kasa ya yi zaben kuma ya nemi yinshi cikin lumana.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:55 0:00

XS
SM
MD
LG