Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Matsayi 3 Na Kungiyar Dattawan Arewa


Batun gudanar da zabe wanda yaki ci, yaki cinyewa shine lamarin da kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta dauki matsayi akai, musamman ma saboda dage zabe da akayi, kuma ake shirin yinsa ran 28 ga wata mai kamawa. Kakakin majalisar Farfesa Ango Abdullahi ya gayawa Muryar Amurka matsayin kungiyar, a hira da yayi da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammed.

“Muna so mu jaddada matsayi uku wadda muka dauka, tun wannan lokaci, har zuwa yanzu”, inji Farfesa Ango Abdullahi.

“Matsayi na farko shine, dole, dole ayi zabe na wannan shekara 2015 irin yadda tsarin mulki ya ajje. A baiwa jama’ar kasa dama su zabi shugabanninsu.”

“Matsayi na biyu shine har yanzu tsarin mulki ya ce ranar 29 ga watan biyar, na wannan shekara (2015), dole a samu gwamnatoci sababbi, a kasa baki guda, da jihohi ranar 29 a sakamakon, ina kara karfafa wanna, a sakamakon zabe wanda za’a yi, a tabbatar da cewa wadannan sababbin gwamnatoci da za’a yi a kasa da Jihohi, za’a yi su da yawun mutanen da suka zabe su.”

“Na uku, mun tsaya akan cewa baza mu taba yadda, da wata gwamnati wadda ba zababbiyar gwamnati bace, a wannan shekarar” a cewar Mr. Abdullahi.

Farfesa Ango Abdullahi bai bayyana matakan da kungiyar zata dauka ba, idan aka karya wannan matsayi da kungiyar da yake wakilta ta dauka.

Kura ta turnuke, tun bayan dage babban zaben kasa baki daya a Najeriya, wanda yanzu haka ake shirin yinsa ran 28 ga watan Maris.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG