Mata a jihar Nasarawa sun ce a shirye suke su fita su yi zabe duk da irin barazanar tsaro da ake yi musu.
Wakiliyarmu Zainab Babaji wacce ta zanta da mata da dama a birnin Lafiya, babban birnin jihar ta ruwaito cewa matan sun kudari aniyar fita su kada kuri’unsu ne domin su karbi ‘yan cinsu.
“Wallahi in za a sake bam ta kasa da sama sai mun yi zabe.” In ji Hajiya Bar'atu Sa'adu.
Ta kara da cewa mata da yawa sun rasa mazanjensu sakamakon hare-hare da aka kai a wasu sassan arewacin Najeriya ta na mai cewa lokaci da mata za su fito su nuna himmarsu a lokacin zabe.
Ita kuwa Rukayyatu Muhammad cewa ta yi duk da cewa gwamnatin ba ta cika alkawarin da ta yi wajen samar da kayayyakin more rayuwa, za su fita su kada kuri'unsu.
A kwanakin baya ne kungiyar da aka fi sani da Boko Haram wacce ke ta da kayar baya a arewacin kasar ta yi gargadin cewa kada kowa ya fita a lokacin zabe mai zuwa domin za ta kai hare-hare.
Wannan kira ya biyo bayan wani yunkuri da kungiyar ta yi na karbe ikon garin Gombe lamarin da ya cutura.
Kungiyar ta Boko Haram ta rasa wasu yankunan da ta kama a 'yan watannin baya bayan da dakarun hadin gwiwa da suka hada da na Najeriya da Chadi da Kamaru suka kai musu hare-hare.