Hukumar zaben Najeriya tace batun cire shugaban ta Farfesa Attahiru Jega labara da suka jima suna jin jita-jita akai kamar yadda mai Magana da yawun hukumar ya shaidawa Bello Habbeb Galadanchi a hirar da suka yi.
Yace su a hukumar zabe ko akwai wannan batu su basu da masaniya, dun a bisa abinda ke faruwa tun wata guda daya wuce har zuwa yanzu ba jita-jitan da ba a yadawa, wani zubin ma sai ace shi Farfesa Jega yayi murabus, har ma a yanar gizo anje an buga wata wasikar bogi ga shaidar cewa yayi murabus da makamantar su.
Muna jin wadannan amma ba wani tushe a cikin wannan jita-jitan, abinda yasa na fadi haka shine kawo yanzu muna muna aiki gadan-gadan anan hukumar zabe kuma ma muna kokarin inganta zabubbukan da zamu yi a wannan wata, saboda haka ma wannan abu yana zama muna kamar jita-jitan ne kamar yadda na fada.
Kuma idan ka duba bisa ga kundin tsarin mulki sashi na 157 inda kundin tsarin mulki ya zana matsayin hukumar zabe karara da kwamishinoni na tarayya, yadda za a iya cire su shine idan mutum yayi murabus da kanshi, ko kuma an same shi da laifi, sailin nan laifin an gurfanad dashi a gaban majilisar tarayya ita ma majilisar tarayyar ta gamsu da cewa shima yayi wannan laifin shine zata ce ya sauka.
Sai kuma idan yana da rashin lafiya mai tsanani wanda zai iya hana shi wannan aikin to wadannan kaidojin kamar yadda aka zana a kundin tsarin mulki, bisa ga wannan ne shugaban hukumar zabe ko kuma kwamishina na zabe zai iya barin aiki kawo yanzu duk wadannan basu taso ba.