Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohin da ke shiyar Arewa maso gabashin Najeriya da ita ma ta yi fama da matsalar tsaro wanda ko a shekarun baya sai da mayakan Boko Haram suka kai hari kan makaranta maza da ke garin Buni Yadi, inda aka hallaka dalibai da dama.
Sannan kuma suka sake kai wani harin a jihar, inda suka kwashe 'yan matan makaranta na Garin Dapchi wanda daga bisani aka dawo da wasu, ban da guda daya mai suna Leah Sharibu da aka bayyana cewa, 'yan kungiyar Boko Haram da su ka sace su, sun ki sakinta domin ta ki ta Musulunta.
Hukumomin jihar sun ce ba za su bari a kuma awon gaba da dalibai a jihar ba don sun gani a baya.
Wasu al’ummar jihar suna ganin cewa ba irin wannan matakai na rufe makarantu ya kamata ace an dauka ba ganin cewa akwai karancin Ilimi a jihar Yoben kuma yana sake mai da harkokin karatu ne baya.
Daya daga cikin iyayen daliban da lamarin ya shafa, Alhaji Sale Bakuro, ya ce akwai 'ya ‘yansa guda hudu a makarantar kwana wanda aka tura su zuwa gida sakamakon wannan umurni da gwamnatin ta bada.
Sai dai mai bawa gwamnan jihar Yobe Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Alhaji Mohammed Mamman, ya ce ai gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah kuma ba za su bari a sake shammatar su ba don a baya sun gani a kwaryar tuwon su.
Ko a makon da ya wuce gwamnatin jihar Zamfara ta bada umarnin rufe dukkan makarantun kwana a jihar sakamakon sace dalibai mata sama da 300 a jihar.
Ita ma jihar Kano ta bada makamanci irin wannan umarni na rufe makarantun kwana da ke wajan birnin Kanon guda 10 saboda tsoron kawo musu hari.
Wadannan al’amura na faruwa ne bayan da ‘yan bindiga suke zuwa makarantun kwana sun sace dalibai domin nema kudin fansa daga wurin gwamnatocin jihohi.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5