A baya hukumar ta musanta kama shi bayan wasu sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter yana mai sukar gwamnatinsu ta APC da shugaba Buhari kan gazawar da suka nuna wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A sakon na Twitter wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Yakasai ya nemi gwamnatin Buhari da ta yi murabus “idan ba za ta iya ba.” Ko da yake tuni an riga an goge sakonnin.
Yakasai ya yi batan-dabo tun bayan da ya wallafa sakonnin, inda aka yi hasashen ko hukumar ta DSS ce ta kama, amma ta ce ba ita ba ce.
Amma kafafen labaran Najeriya da dama musamman na internet a daren ranar Asabar sun ruwaito kakakin hukumar Peter Afunanya cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai cewa Yakasai na hannunsu.
Cikin sanarwar, ya ce ana bincikensa ne kan wasu batutuwa da dama ba wai akan ra’ayin da ya bayyana a kafafen sada zumunta ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kalaman na Yakasai na Twitter martani ne kan sace ‘yan makarantar Jangebe da ‘yan bindiga suka yi a ranar Juma’a a jihar Zamfara inda ya nuna gazawar gwamnatin a cewar jaridar Daily Nigerian.
Dalibai sama da 300 ‘yan bindigar suka kutsa da su cikin daji sa’o’i gabanin sako daliban makarantar Kagara da su ma aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a jihar Neja.
A halin da ake ciki gwamnatin ta Kano ta sallami Yakasai daga bakin aiki biyo bayan wannan rubutu na shi.
Wannan ba shi ne karon farko da Yakasai wanda aka fi sani da @dawisu a Twitter yake sukar gwamnatinsu ta APC ba, wacce ita ke mulki a Kano karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ya taba sukar Buhari kan zanga zangar Endsars da ta mamaye wasu sassan kasar lamarin da ya sa har aka dakatar da shi daga aiki.
Karin bayani akan: DSS, Salihu Tanko Yakasai, Nigeria, da Najeriya.