Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Lahadi Masarautar Kano Za Ta Jagoranci Mukabalar Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano


Mai Martaba Aminu Ado Bayero Sarkin Kano
Mai Martaba Aminu Ado Bayero Sarkin Kano

Ana shirye-shiryen gudanar da mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman Kano da ke arewacin Najeriya.

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da ranar 7 ga watan Maris na wannan shekara, a matsayin ranar da za ta gudanar da mukabalar.

Kwamishinan yada Labaran jihar Kano Muhammad Garba ne ya shaidawa Muryar Amurka a yau.

Ya ce, malaman jihar ke da alhakin shirya wannan mukalabar, inda gwamnatin jihar ta shigo ciki, shi ne wajen samar da hanyar tabbatar da yiwuwar hakan, ta hanyar samar da wuri da lokaci da dawainiyar malamai.

Garba, ya kara da cewa za’a gudanar da mukabalar ne a fadar mai Martaba Sarki Kano - malamai kuma a nasu bangaren tuni suka gama shirinsu, inda shi ma Shehin Malami Abduljabbar Nasiru Kabara, tuni aka mika mishi takardar sanar da shi taron kuma ake sa ran ya gama shiri.

Malaman dai sun zabi wadanda za su zauna da shi, inda yake cewa taron ba zai wuce na mutane 35-40 ba.

Haka zalika, gwamnati za ta tabbatar da an saka mukalabar a gidajen radiyo domin al’ummar gari su ji yadda mukalabar ke wakana.

Idan masu sauraron na biye da mu a ranar 7 ga Fabrairun wannan shekara ne gwamantin Kano, ta dakatar da malamin daga gudanar da karatu a makarantarsa saboda da zarginsa da yin batanci ga Annabin (S.A.W.,) zargin da ya musanta.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG