Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10 A Jihohin Kaduna Da Sokoto


Arrested Armed Bandits in Zamfara State
Arrested Armed Bandits in Zamfara State

‘Yan bindiga sun kai hari a kauyuka 3 da ke cikin kananan hukumomin mulkin Igabi da Kajuru na jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 7.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta tabbatar da kai harin a garuruwan Kajinjir da Rago a karamar hukumar Igabi inda aka kashe mutum 4 tare da raunata wani mutum daya,.

Sannan sai wani harin da aka kai da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 3 a garin Katuru da ke cikin karamar hukumar mulkin Kajuru.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce daga cikin wadanda aka kashe an gano wani mai suna Ibrahim Rabi’u da wani Abdulrahman Mohammed, yayin da Kamal Murtala da ya sami rauni kuma yake karbar kulawa a asibiti.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai

A jihar Sokoto kuma wasu ‘yan bindigar sun kai wani hari a garin Gatawa da ke cikin karamar hukumar mulkin Sabon Birni, inda suka kashe mutum 3, ciki har da wani yaro dan gudun hijira mai shekara 7.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani da shaida lamarin yana cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na daren Asabar, suka kuma ci gaba da harbe-harbe har zuwa karfe daya na safiyar jiya Lahadi, sa’ar da sojoji suka isa wajen.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun na Najeriya sun yi musayar wuta da su, amma wadanda suka shaida lamarin sun ce ba su ga gawar ko daya daga cikin ‘yan bindigar ba, domin “sukan tafi da ‘yan uwansu ne ko da an kashe su.”

Wadansu 'yan bindiga da aka kama a Zamfara
Wadansu 'yan bindiga da aka kama a Zamfara

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga a arewacin Najeriya ta zama ruwan dare, inda zai yi wuya a kwashe mako guda ba tare da an kai hari a nan da can ba.

A mafi akasarin lokuta, maharan kan yi garkuwa da mutane don neman kudin fansa, inda wani lamari na baya-bayan da ake yawan gani shi ne hari da suke kai wa makarantun kwana don sace dalibai.

Yanzu haka akwai dalibai ‘yan mata sama da 300 da ‘yan bindigar suka sace a yankin Jangebe na karamar hukumar Talatar Mafara da ke jihar Zamfara, wadanda har yanzu ba a sako su ba.

Ko da yake, gwamnatin jihar ta Zamafara ta ce tana gab da karbo daliban wadanda ‘yan binidgar suka far wa makarantarsu da sanyin safiyar Juma’ar da ta gabata.

Wannan lamari ya janyo suka daga ciki da wajen Najeriya, lura da cewa ya zama ruwan dare inda mutane kan nuna mamakin yadda za a sace daruruwan dalibai a shiga da su daji.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar a ranar Juma’a, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gargadi ‘yan bindigar da su shiga taitayinsu yana mai cewa ana raga musu ne kawai saboda bin ka’idoji yaki da ake yi.

Sanarwar ta ce, hukumomin Najeriya na kokari ne su kare lafiyar mazauna yankin da ‘yan bindigar suke da kuma wadanda ake garkuwa da su, amma in ba haka ba da tuni an kawar da su.

Yayin da wasu gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya ke kokarin yin sulhu da ‘yan bindigar, gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta ce ba ta da niyyar yin hakan.

Karin bayani akan: jihar Sokoto, jihar Kaduna, Muhammadu Buhari​, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG