Gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya ziyarci makiyayan da aka kaiwa hari, a wasu kauyukan Bachama, na karamar hukumar Numan da ke kudancin jihar wanda yanzu haka ke kwance a asibitin kwarararru dake Yola,wato Yola Specialist Hospital.
Gwamnan wanda yayi kwalla, sakamakon abin da ya gani na irin harin gillar da aka yi, yace gwamnati ba zata kyale duk wani dake da hannun a ta’addancin ba, sa’annan kuma ya bayyana taimakon da gwamnati zata yiwa wadanda ke kwance a gadon asibiti.
Shugaban asibitin kwararrun Dr Bala Sa’idu, ya bayyanawa gwamna cewa wadanda aka kawo na samun kulawar da ta kamata.
Sai dai yayin da gwamnatin jihar ke shirin kaddamar da kwamitin bincike, wata sabuwa ta kunno kai inda hadakar kungiyar al’ummar yankin Bachama, da akewa lakabi da Numan Federation Alliance Group, ta fitar da wata sanarwa dake dauke da sa hannun shugabanta Mr Vakai Ndagoso, inda ta alakanta kisan ‘ya’yan makiyayan da rashin aiwatar da rahoton bincike da gwamnati jihar ta kafa kan abubuwan da suka faru watannin baya a karamar hukumar Girei.
Haka nan ma kuma kungiyar ta bukaci ‘yan majalisar dokokin jihar su gaggauta kafa dokar hana kiwo kamar yadda wasu jihohi suka yi.
Daga Yola, ga rahoton da Ibarhim Abdul'aziz ya aiko man.
Your browser doesn’t support HTML5