Bayanai na nuna cewa dan majalisar wakilai dake wakiltar al’ummomin yankin Michika da Madagali, Adamu Kamale ya nemi ya bi jirgin tawagar hukumar bada agajin NEMA mai saukar ungulu, to amma sai dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Senata Abdul’Aziz Nyako, wanda ke zama shugaban kwamitin aiki da cikawa na majalisar kuma mai sa ido kan harkokin hukumar NEMA, ya ce dan majalisar wakilan ya sauka saboda babu sunansa a jerin wadanda zasu kai kayayyakin tallafin, batun da ya harzuka dan majalisar.
A wata takardar koke da ya rabawa manema labarai a Yola, dan majalisar ya zargi Sanata Abdul’Aziz Nyako da cin zarafinsa, da kuma hana shi sa ido game da kayayyakin da za a kai mazabarsa, abin da ya ce ba za ta sabu ba.
Sai dai Sanata Abdul’Aziz Nyako, ya musanta zargin, inda yace dan majalisar Adamu Kamale gayyar sodi ne da yaso ya hallaka kansa.
Bashir Idris Garga shine babban jami’in hukumar ta NEMA mai kula da jihohin arewa maso gabas, ya bayyana cewa babu sunan sanata Adamu Kamale a cikin jerin sunayen tawagar da za ta kai kayayyakin saboda bai bada sunansa ko na wakilinsa akan kari ba.
Wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdul’aziz na da karin bayani a cikin sauti.
Facebook Forum