Yayinda yake gabatar da jawabi a wajen taron shugabannin kasashen yankin gabar Tekun Guinea, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya maida hankali akan batutuwan da suka shafi tsaro da hadin kai.
Farfesa Osinbajo yayi ga kira shugabannin kasashen da su sabunta kokarinsu wajen sake sabunta kuzarin hukumar gabar tekun Guinea domin ta zama abokiyar tafiya a duka kokarinsu a matakin kasa, shiya ko kasa da kasa. Hakan zai sa a tabbatar da tsaro, da samun zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa ga kasashensu da jama’arsu da sauran masu ruwa da tsaki a shiyar, inji Farfesa Osinbajo.
Yanzu Najeriya ta karbi jagorancin kungiyar mai kasashe takwas daga Jamhuriyar Guinea.
A wajen taron, harkar tsaro ce take bakin duk wadanda suka yi jawabi
Manjo Janar Babagana Monguno mai ba shugaban Najeriyashawara akan harkokin tsaro yace Najeriya ta ci gaba da karfafa sojojinta musamman mayakan ruwa domin tunkarar duk wani kalubalen tsaro.
Babbar sakatariyar hukumar Tekun Guinea Uwargida Adenike Ogunko ta nemi hadin kan kasashen dake cikin kungiyar, da su cika alkawuransu na bada kudaden karo karo domin samun gudanar da ayyukan sakatariyar kungiyar
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum