Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta kaddamar da wani shirin da zai habaka cimaka a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno domin kaucewa yiwuwar karancin abinci a yankin a badi kamar yadda bincike ya nuna.
Shirin hukumarwanda ta kaddamar a Maiduguri, jihar Borno, ya hada da bunkasa noman rani ta hanyar bada irin shinkafa da dawa da masara da kuma irin kayan miya. Za’a rabawa manoman rani da suka fito daga kananan hukumomi 16.
Shugaban hukumar abincin dake Najeriya, Mr Koroma, ya ce hukumar na shirin tallafa wa mutane dubu 700 da suka fito daga jihohin Borno da Adamawa da sansanonin ‘yan gudun hijira. A cewarsa a jihar Borno kawai mutane kimanin 270,000 ne za su amfana da tallafin a kananan hukumomi 16.
Za’a ba manoman irin kayan miya da na shinkafa da taki da famfunan ban ruwa da wasu kayayyakin noma da za su yi amfani dasu a gida.
Har wa yau, a karkashin shirin za’a raba wa matasa shanu 400 domin su zama hanyar dogaro ga kai. Mata ma za’a raba masu awakai 6,600 domin inganta rayuwarsu, da inganta cimaka da karfafa tsaro musamman tsakanin mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabashin Najeriya.
Mr. Koroma ya ce manufar shirin nasu shi ne habaka harkokin noma ga mutanen da rigingimu suka tagayyarar da su.
Akan dalilin da ya sa gwamnatin iihar Borno ta hada gwuiwa da Majalisar Dinkin Duniya, gwamnan jihar ya ce da suka fara fuskantar karancin abinci sun kai kuka wa shugaban kasa wanda ya taimaka aka shawo kan matsalar sai dai ya hada da cewa haryanzu akwai matsala saboda mutane da yawa ba su yi noma ba. Gwamna Shettima ya ce mutane na son komawa gidajensu saboda haka wajibi ne a san na yi domin su samu abinci.
Dangane da noma ko tanadin kayan noma Gwamna Shettima ya ce babu wata jiha a Najeriya da ta yi abun da suka yi. Injishi kayan na nan kuma da zara mutane na komawa yankunansu za’a bisu da kayan.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum