Gwamnan ya gudanar da jawabi na musamman ga al'ummar jihar ta kafofin yada labarai inda ya yi masu godiya saboda damar da suka bashi har na shekaru takwas ya mulkesu.
Ya yabawa jama'a da gudanar da zabukan a cikin kwanciyar hankali da lumana. Sakataren gwamnatin jihar Idris Ndaku ya kara haske akan jawabin gwamnan. Yace gwamnan ya roki 'yan jama'iyyarsa su karbi sakamakon zaben kana su cigaba da rayuwarsu ta yau da kullum su jira gaba. Duk wanda ya zo su bada goyon baya domin cigaban jihar.
Ahalin yanzu masu neman mukami na yin tururuwa zuwa gidan gwamna mai jiran gado Abubakar Sani Bello wanda tuni ya gayawa al'ummar jihar su sa ran ganin kyakyawan shugabanci.
Mahaifin sabon gwamnan tsohon gwamnan soji na jihar Kano Kanar Sani Bello yace zai yi farin ciki matuka idan har gwamnatin dansa ta yiwa al'ummar jihar shugabanci mai adalci. Inji Kanar Sani Bello sabuwar gwamnatin zata gaji abubuwa da dama kamar bashi da talauci da ayyuka da dama da ba'a yi ba da wasu matsaloli.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5