A wani abun da ba'a saba gani a Najeriya ba gwamnan Ekiti Dr. Fayemi wanda ya sha kaye a zaben da aka yi karshen makon jiya ya taya abokin takararsa Ayo Fayose murna.
WASHINGTON, DC —
Ranar Asabar da ta gabata aka yi zaben gwamnan jihar Ekiti tsakanin gwamna mai ci yanzu Dr. Kayode Fayose na jam'iyyar APC da Ayo Fayose na jam'iyyar PDP.
A wani abun da ba'a saba gani a Najeriya ba gwamna Kayode Fayemi wanda ya sha kaye a zaben karshen mako ya taya abokin takararsa Ayo Fayose murna dangane da nasarar da ya samu. Kayode Fayemi wanda ya zama na biyu a yawan kuri'u ya yiwa Ayo Fayose mai jiran gado murna ta kafofin gidajen telibijan da radiyoyin jihar. Yace nasarar da Ayo Fayose na jam'iyyar PDP ya samu bai bashi haushi ba domin zabin da 'yan jihar Ekiti suka yi ke nan.
Gwamnan mai barin gado yace ya tattauna da sabon gwamnan mai jiran gado Ayo Fayose a lokacin da ya yi masa barka da samun nasara a matsayin zababben gwamnan jihar Ekiti. Yace nan gaba kadan zai sake yin magana da Ayo Fayose domin su tsara yadda za'a mika masa mulkin jihar Ekiti. Yace jami'an tsaron Najeriya sun mamaye jihar domin haka zasu yi nazari akan lamarin.
A cikin watan Oktoba ne sabon gwamnan Ayo Fayose zai kama madafin ikon jihar lamarin da zai sake mayar da jihar karkashin PDP.
Kafin zaben mutane da yawa sun bar jihar domin tsoron yin gumurzu tsakanin magoya bayan jma'iyyun biyu, wato APC da PDP. To amma an yi zaben lami lafiya ba tare da wani hargitsi ko tashin hankali ba.
Shi ma Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya taya sabon gwamnan Ayo Fayose murnar cin kujerar. Yace nasararsa ta ba mara da kunya.
Alhaji Yaro Mai Nama na Ado Ekiti daya daga cikin masu goyon bayan gwamnan da ya sha kaye, Kayode Fayemi, yace yadda gwamnan mai barin gado ya taya Ayo Fayose murna tayi kyau. Yace duk zaben daga farko har karshe a gabansu aka yi. Idan za'a yi zabe kamar yadda aka yi a Ekiti koina a kasar da komi yayi dadi.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5