Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaben Gwamna a Ekiti


‘Yan sanda suna daukan samfuri a inda aka kai harin bom da mota a Nyanya.
‘Yan sanda suna daukan samfuri a inda aka kai harin bom da mota a Nyanya.

Da sanyin safiyar Asabar dinnan ne dubban daruruwan masu kada kuri’a a Jihar Ekiti suka fita zuwa rumfunan zabe

NAJERIYA - Da sanyin safiyar Asabar dinnan ne dubban daruruwan masu kada kuri’a a Jihar Ekiti suka fita zuwa rumfunan zabe, domin tantance sunayensu domin kada kuri’u, ga wanda zai zama gwamnan Jihar Ekiti.

Jamilu Adamu dake kan layi yayi karin bayani akan aikin jefa kuri’un. “Tun misalin karfe 8 da rabi na safe nake kan layi, abun babu wahala.”

NAJERIYA - Yayinda dambarwar tsige gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako da mataimakinsa ke daukan wani sabon salo, yanzu haka wasu kusoshin jam’iyyar PDP dake Abuja sun tabbatar da cewa da yawunsu ne ‘yan majalisar dokokin Jihar ke son tsige gwamnan da mataimakinsa Bala John Ngilari.

Dr. Umar Ardo wani kusa ne a jam’iyyar ta PDP.

“Su (‘yan majalisar) zo wajena, sunce mun suna zuwa wajen iri na, iri na, ban san da wa, da wa, da wa suka je, suka gani ba. Amma sunzo wajena, munyi magana da su, munyi magana da su. Sun gaya mini abunda suke ciki, ni kuma na gaya musu ra’ayina akai. Bai kamata Nyako yana gwamna da Ngilari ba.”
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG