Gwamnan jihar Murtala Nyako ta bakin daraktan yada labaransa Malam Muhammed Sajoh yace kwace asusun jihar tamkar manuniya ce cewa da yawun fadar shugaban kasa ake kokarin tsige gwamnan. Duk dambarwar da ake yi ba domin a kyautatawa mutanen jihar ba ne amma domin a tozarta masu a kuma gallaza masu ne. Yace tattalin arzikin jihar ya ta'alaka ne akan hada-hadar gwamnati. Idan ba'a biya albashi ba da 'yan kwangila tattalin arziki zai kara tabarbarewa, 'yan kasuwa ma zasu ji a jikinsu.
Ya cigaba da cewa duk dambarwar da a keyi ta son zuci ne. Ana kokarin a yi abu mai kama da juyin mulki, a dora wadanda ake so su zama shugabanni.
Amma jam'iyyar PDP ta bakin sakatarenta Barrister A.T. Shehu yace kwace asusun gwamnatin jihar da yunkurin tsige gwamna da mataimakinsa duk sun yi daidai. Gwamnan jihar ya karbi kudade sama da nera biliyan saba'in amma ba'a ga abun da yayi da kudaden ba. Duk masoyin Adamawa yana murna idan gwamnan zai tafi ta hakan.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.