Ana ba wadanda suka yi fice wajen yada muradun shirin gyara tattalin arziki na shugaba Jonathan. Mrs. Sarah Jibirin tace mu kudura a zukatanmu cewa zamu canza kuma zamu iya gyara lamuran Najeriya musamman ta hanyar dabi'u nagari dake kunshe a duka addinai.
Taron da cibiyar bada lambobin girma ga lamuran shugabanci mai zaman kanta ta shirya nada nasaba da yadda kungiyoyi daban daban suke bayyana domin yada manufofin gwamnatin Jonathan da dalilan da suke gani ya dace PDP ta cigaba da mulki a 2015.
Ambassador James Bature dake da kungiyar taimakawa marayu da miskilai daga jihar Neja yana cikin wadanda suka amshi kyautar da nuna damuwa da abun da ya kira garambawul da PDP ke bukata a Neja idan ana son cimma nasara. Yace wanda mutane suna so a soshi. Amma yanzu ko kana kisa idan ka fita PDP akwai munafukai da zasu bika. Yace matsalar PDP a Neja ke nan. Yakamata a zauna a fadawa juna gaskiya domin babu jittuwa da taimakon juna. Mutane sun gaji.
Adamu Yaro Gombe wanda bai yi zurfi a ilimin boko ba yana tsakiyar 'yan bokon da suka karbi lambar girma. Yace duk aikin da mutum ya tsaya ya kware akai ya isa mutum cin abinci. Ba zunzurutun boko ba ne nasara a rayuwa. Abun da ake bukata shi ne mutum ya zama adali mai kyautatawa jama'a da fadin gaskiya ba tare da cin mutuncin mutane ba.
Ga karin bayani na Nasiru Adamu El-Hikaya.