Kungiyar ta nuna bacin ranta da abun da ta kira shishshigin da gwamnan keyi akan mulkin shugaba Jonathan yayin taronta a Abuja. Tace hakan bai taimaka wurin dawo da zaman lafiya ba a jihar.
Tsohon kantoman jihar Filato Aircommodore Dan Suleiman shi ne shugaban taron da aka gudanar a Abuja. Yace basu yadda da maganar da gwamnan yayi ba domin maganar bata da kyau. Misali, gwamnan yace tashin hankalin da 'yan Boko Haram keyi a arewa maso gabas, wai Jonathan ne ke haddasa shi da sojojin kasar.
Shugaban kungiyar ya kira gwamnan ya gyara zamansa. Rashin juttuwa da shugabannin PDP yasa gwamnan ya canza sheka zuwa APC.
Dangane da zaben 2015 Dan Suleiman yace babu shakka suna son PDP ta kwace mulkin jihar a zabe mai zuwa.
A gefe guda kuma jam'iyyar APC ta nuna damuwa da abun da take gani bita da kulli ne ga nasarar adawa akan gwamnati mai ci. Mai Mala Buni sakataren APC na jihar Adamawa yace shure-shure ba ya hana mutuwa. Gwamnatin Najeriya tana barin ana yiwa mulkin dimokradiya karan tsaye.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.