Gwamnan Borno Zai Kori duk Wanda Ya Karkata Abincin 'Yan Gudun Hijira

Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

Gwamnan jihar Borno Alhaji Ibrahim Shettima ya yi barazanar korar duk wani kwamishana ko shugaban karamar hukuma da aka kama yana karkata abincin da aka tanadawa 'yan gudn hijira

Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin jihar dake birnin Maiduguri yayinda yake rantsar da shugabannin kananan hukumomi 27 da sabbin kwamishanoni 21.

Gwamnan yace ashirye yake ya kori kowane kwamishana ko shugaban karamar hukuma da aka kama yana karkata dukiyar jama'a.

Kodayake gwamnan ya nemi gafara amma ya tabbatar masu cewa zai taka kafafuwan mutane da yawa akan wawure kayan jama'a da yin almubazaranci.

Kazalika gwamnan ya umurci shugabannin kananan hukumomin Gamboru Ngala da Gwoza da Kalabarge da su kwashe kayansu su koma garin Yola inda yace akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu goma daga jihar Borno. Shi ma gwamna Ibrahim Shettima yace zai ziyarcesu ranar Litinin mai zuwa idan Allah ya yadda a kokarin maidasu jihar Bornon.

Gwamna Ibrahim Shettima yace dole ne shugabannin su sayi kayan abinci wa mutanensu dake mutuwa. Ya kara cewa kowane kwamishana ko shugaban karamar hukuma ko dan majalisa na jiha ko tarayya da ya taba abincin zai fuskanci fushin hukuma.

Gwamnan yace da zara an gama sallah zasu fara sake gina garin Bama ko da taimako daga waje ko babu. Gwamnan ya kara da cewa duk wadanda rikicin ya daidaita zasu sake gina masu makarantunsu da asibitocinsu da ma gidajensu.

Shugaban karamar hukumar Gamboru Ngala Abdulrahaman Abdulkarim yace da ma suna jiran irin wannan umurnin ne daga gwamnan jihar na cewa su tare a Yola har sai an kwashe 'yan asalin kananan hukumominsu zuwa garuruwansu kafin su koma.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Borno Zai Kori duk Wanda Ya Karkata Abincin 'Yan Gudun Hijira