'Yan Boko Haram sun kwashe fiye da shekaru biyu suna mamaye da garin Gamboru Ngala.
Mazauna yankin su fara bada shawarwari akan yadda garin ba zai sake fadawa hannun 'yan ta'adan Boko Haram ba. A yankin dai 'yan Boko Haram sun taba kwace garuruwa har guda ashirin a cikin jihar Borno. Lamarin ya sa dubun dubatan mutane suka yi gudun hijira zuwa wurare daban daban har da kasashen Nijar da Kamaru.
Yanzu al'ummar garin sun kira gwamnati ta gina barikin soja na dindindin a garin nasu saboda kada garin ya sake fadawa hannun 'yan Boko Haram ganin yadda suka yi kakagida a yankin da yadda suke yawan dawowa koyaushe aka fatattakesu.
Gamboru Ngala gari ne da yake kan iyaka da wasu kasashen Afirka kuma cibiyar kasuwanci ne na kasa da kasa.
Wani yace ana bukatan sojojin ne domin su dinga shiga kauyukan yankin saboda tabbatar da cewa an kakabe 'yan ta'adan basu kuma samun wurin sake kafa sansani ba.
Banda bukatar gina barikin soja, al'ummar garin dake gudun hijira na son a sake gina masu gidajensu da 'yan ta'adan suka rushe ko konesu mururus.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.