Shugaban kwamitin Farfesa Sunday Ochoche ya bayyana cewa, gidauniyar taba asibitoci biyu a jihar Borno da suka hada da asibitin kwararru da kuma asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, naira miliyan ashirin kowannensu a lokacin da kwamitin ya kai ziyara jihar kwanan baya, domin taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya raunata da suke karbar magunguna a wadannan jihohi.
Farfesa Ochoche yace akwai aiki a gaban gidauniyar tukuru na sake gina gidajen wadanda rikicin kungiyar Boko Haram ya shafa, yace a wannan ziyarar da suka kawo, suna da adadin mata masu juna biyu dari hudu da goma wadanda zasu ba naira dubu goma kowannensu domin su iya kula da kansu yanzu da kuma bayan sun haihu.
Yace baki daya, gidauniyar tana shirin taimakawa mata dubu uku ne a jihar Borno kawai, matan da suka sami tallafin sun bayyana cewa, zasu sayi ragunan suna da kuma muhimman kayayyakin bukata daga cikin tallafin da aka basu.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga jihar Borno, Najeriya.