Al'ummar Borno suna cigaba da kasancewa cikin duhu duk da farin cikin da wasu su keyi na ingantakar wutar lantarki a nasu yankin tun lokacin da Buhari ya dare kan mulkin Najeriya.
Al'ummar Borno sun ce su labarin wadatuwar wutar suke ji har yanzu domin wadatar bata iso wurinsu ba. Babu wani sauyi.
Fiye da shekara guda ke nan da al'ummar jihar musamman mazauna cikin Maiduguri babban birnin jihar suka kasance cikin duhu sakamakon lalata wutar da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi musamman a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri. Tun a lokacin mazauna yankunan suka rabu da samun wuta.
Amma shugaban hukumar samarda wutar lantarki na shiyar arewa maso gabas Injiniya Idris Lawal Alim ya yi tattaki zuwa jihar tare da ziyartar fadar gwamnatin jihar inda ya yiwa gwamnan jihar alkawarin kawo karshen matsalar. Yayi alkawarin magance matsalar nan da nan.
Injiniya Alim yace daga yankin ya fito yaya kuma za'a ce Maiduguri bata da wuta. Yace dalili ke nan da ya ziyarci jihar domin bada tabbacin maidowa birnin wutar lantarki.
Dangane da sauran kasar Injiniya Alim yace koina a kasar akwai wuta. Wanda bai yini da wuta ba to zai kwana da ita.
Tun farko gwamnan jihar Ibrahim Kashin Shettima ya roki hukumar ta yi duk iyakacin kokarinta ta dawowa jihar wutar lantarki. Gwamnan yace masana'antu ba zasu yi aiki ba sai da wuta. Ana bukatar wuta a gidaje. Haka ma masu kananan sana'a na bukatan wuta. Gwamnan ya yi alkawarin bada duk taimakon da ake bukata na dawo da wutar.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.