Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna a Najeriya ya nada Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarkin na 19 Zazzau

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Nasiru El-Rufai na jahar Kaduna ya nada Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarkin na 19 Zazzau. An Haifi Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ne a ranar 8 ga Yuni, 1966 a Zariya, mahaifinsa, Nuhu Bamalli ne ya rike Magajin Garin Zazzau kafin a sauya masa sarautar.