Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Zazzau Shehu Idris Ya Rasu


Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris

Sarkin masarautar Zazzau a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya mai martaba Alhaji Shehu Idris ya rasu. Ya rasu yana mai shekara 84.

Rahotannin daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa Sarkin masarautar Zazzau Mai Martaba Alhaji Shehu Idris ya rasu.

Dan Isan Zazzau Umar Shehu ne ya tabbatar wa da Muryar Amurka cewa, Sarkin ya rasu ne a asibitin 44 Barrack da ke Kaduna, bayan fama da ya yi da rashin lafiya.

A watan Fabrairun wannan shekara ne Sarkin ya yi bikin cika shekara 45 akan karagar mulki.

"Cikin wadannan shekaru 45, an samu canje-canje iri-iri, saboda haka muna fata wadannan canje-canje za su zama abin tarihi." In ji marigayi Sarkin Zazzau yayin wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikara a watan Fabrairu.

A shekarar 1975 Sarki Shehu Idris ya hau karagar mulki bayan rasuwar Sarki na 17 Muhammadu Aminu. Ya rasu ya bar 'ya'ya 38.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG