Dr. Ahmed Abubakar Gumi wanda ke kan gaba wajen ceto daliban kwalejin ya shirya walimar taya daliban murna tare da karfafa su kuma ya ce za su cigaba da irin wannan kokari. Ya kuma kara da cewa ba za su ja baya ba da yunkurin ganin a ceto dukkan yaran da aka sace.
Tsohon Shugaban hukumar inshoran lafiya na Kasa, farfesa Usman Yusuf na cikin wadanda su ka yi jawabi wurin wannan taro kuma har sai da ya zubda hawaye yayin da ya ce kukan na shi na jin dadi ne da kuma rashin jin dadi, ganin cewa yaran nan sun zauna daji har tsawon kwanaki 56 cikin ruwan sama, rana, cizon sauro, kuda da dai sauransu.
Gashi yau Allah ya sa sun fito amma akwai sauran aiki tun da har yanzu akwai sauran yaran Greenfield, ga kuma yaran Cibok da sauran yara da dama.
A cikin hirar su da Muryar Amurka daliban da aka yi garkuwa da su sun bayyana irin wahalar da su ka sha a cikin kwanakin nan 56 da suka hada da doguwar tafiya da rashin wanka, mafi tashin hankali kuma shi ne irin bindigogin da suke dauke da su da suka bayyana cewa, ko wajen sojojin Najeriya, ba su taba ganinsu ba.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5