Fadar shugaban Najeriya, ta ce tana cike da takaici da alhinin sace daliban jami’ar Greenfield da ‘yan bindiga suka yi, kamar yadda iyayen daliban ke ji.
Kalaman fadar na zuwa ne a ranar da ‘yan bindigar suka yi barazanar za su kashe ragowar daliban 17.
Tuni ‘yan bindigar sun riga sun kashe biyar daga cikinsu, yayin da rahotanni ke cewa an saki wani dalibi shi kadai a ranar Talata.
Maharan sun nemi miliyan 100 a matsayin kudin fansa hade da babura 10.
“Muna cikin matukar damuwa tare da jin zafin da iyayen daliban Jami’ar Greenfield ke ji.” Sanarwar wacce fadar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce.
Ta kara da cewa, “gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar sojoji da jami’an tattara bayanan sirri, na aiki don tallafawa gwamnatin Kaduna domin ganin an kawo karshen wannan lamari, ba tare da an sake asarar wani rai ba.”
A ranar 20 ga watan Afrilu aka sace daliban na Greenfield a makarantarsu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
‘Yan bindigar da suka sace daliban jami’ar ta Greenfield sun yi bazaranar kashe su idan har ba a biya masu bukatunsu ba.
Najeriya na fuskantar matsalar satar mutane don neman kudin fansa, wacce ta yi kamari a ‘yan kwanakin nan musamman a arewa maso yammaci.
Baya ga wannan matsala, akwai hare-hare damayakan Boko Haram suka zafafa a arewa maso gabashi da kuma na ‘yan bindiga da suka addabi yankin kudu maso gabashin kasar.