A cewar wasu al'umomin yankin, ba su taba ganin ambaliyar ruwa da tayi masu ta’adi kamar ta wannan karon, domin kuwa ruwan ya mamaye gonaki da gidaje tare da salwantar rayukan da ba a kai ga tantance yawan su ba.
Muhammadu Bello, wani magidanci ne a garin na Gummi, wanda lamarin ya shafe shi, ya ce tun jiya ake ruwa har wayewar safiyar yau, muna ganin ruwa amma ba mu taba ganin irin wannan ba, domin ana yin su kamar da bakin kwarya. Adadin gidajen da su ka rushe sun fi karfin dari shida ko dari bakwai.
Bello ya kara da cewa ambaliyar tayi masu ta'adi a gonakin su, domin gero da suka noma wanda ke dab da nuna ruwan ya mamaye shi, kuma abincin da su ke da shi aje a gida, ruwan ya salwantar da shi.
Shi kuwa Mas'udu Lauwali Birnin Magaji, wanda da ne ga Uban kasar gundumar ta Birnin Magaji a yankin na Gummi, ya ce a yankin nasu na Birnin Magaji dabbobi da gonaki ne aka yi asarar su sosai a yankin.
Mutane da dama sun jikkata, wasu wuraren kuma da dabbobin su ga gonakin su sun yi asarar su. Akwai wasu mutum biyu da farko mun dauka sun mutu, yanzu mun suna da sauran rai sai dai daya ya karye a hannu da cinya, a cewar Mas’udu.
Kantoman karamar hukumar Gummi, Hon. Aminu Nuhu Falale, ya ce sun kadu matuka da faruwar lamarin wanda ya ce tuni gwamnan jihar Dauda Lawal ya ba da umurnin aje ayi wa al'ummar jaje a kuma tantance irin asarar da aka yi.
Sai dai ya zuwa yanzu ba mu samu rahoton mutuwar kowa ba, sai dai lalacewar gidaje, gonaki da sauran su a garuruwan Gayari, Gamo, Daki Takwas, Gwalli, Falale, Iyakar da dai sauran wurare, in ji Falale.
A bangaren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Zamfara kuwa, Daraktan kula da faruwar iftila’i na hukumar, Hassan Usman Dauran, ya ce lamarin sai wanda ya gani domin kuwa nan take ba za’a iya kiyasta yawan gidajen da su ka ruguje ba a cikin garin na Gummi ba.
Hassan ya ce har yanzu ba’a iya gano adadin gidajen da su ka ruguje a nan take, domin suna da yawa sosai, mutane kuma da su ka rasu ance mana 9 wasu kuma sun ce 10, ba mu kai da tantance adadin su ba.
Ya zuwa yanzu dai gwamantin jihar Zamfara ta tura wata tawaga da ta kunshi Kwamishinoni da Kantoma da ‘yan-siyasa, domin jajantawa al'umar yankin da kuma duba yanayin barnar da ambaliyan ruwan tayi.
Saurari cikakken rahoton Abdulrazak Bello Kaura:
Your browser doesn’t support HTML5