Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Mutane 24 Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa Da Zabtarewar Kasa A Ivory Coast


Ivory Coast
Ivory Coast

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a birnin Abidjan gari mafi girma a kasar Ivory Coast sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 24 sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon mako guda, kamar yadda hukumomi suka bayyana a yau Talata

Mutuwa sakamakon ambaliyar ruwa ba bakon abu ba ne a kasar dake yammacin Afirka a lokacin damina, amma a cewar hukumar kula da yanayi ta kasar Ivory Coast, ruwan sama na baya-bayan nan ya yi kamari inda ya kai fiye da milimita 200 (inci 8) a wasu gundumomi wanda ya ninka adadin da aka saba yi a rana daya.

Wasu Matsugunan na fuskantar barazanar zabtarewa musamman saboda rashin magudanar ruwa a tsakanin gidaje wanda galibi ana gina su cikin sauri kuma ba bias ka’ida ba.

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun kuma haifar da "mummunan barna" a duk fadin birnin, inda suka mamaye gidaje da hanyoyi, in ji ofishin kare fararen hula na Ivory Coast.

Sai dai akalla mutane 271 da suka makale bayan afkuwan lamarin amma an yi nasarar ceto su.

A shekarar da ta gabata ne jami’ai suka rusa gidajen da aka gina a gefen wani rafi a birnin Abidjan a matsayin wani mataki na hana afkuwar ambaliyar ruwa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG