Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 21 A Nijar, A Cewar Jami’an Kasar


Ambaliyar ruwa a kasar Brazil
Ambaliyar ruwa a kasar Brazil

A cikin makonnin farko a lokacin daminar bana ambaliyar ruwa ta kashe mutane 21 ta kuma shafi wasu fiye da 6,000 a Nijar, inda ba a cika samun isasshen ruwan sama a wasu sassan kasar ba, a cewar wani jami'in gwamnatin kasar.

Mutane 13 sun mutu a lokacin da gidajensu suka rufta kansu, sannan wasu 8 kuma ruwa ya tafi da su, bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, a cewar Kanar Boubacar Bako, babban daraktan hukumar kare al’uma, ta gidan talabijin na kasar a yammacin ranar Alhamis.

A yankin Maradi da ke kudu maso tsakiyar Nijar, Ali Abdou dan shekaru 35, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AP ta wayar tarho cewa ruwan sama mai karfin gaske ya lalata gidaje a yankinsu, yana mai cewa ruwan farko kenan, amma har gidajensu sun fadi.

Lokacin damina, da ke kankama daga watan Yuni zuwa Satumba, ya kan lakume rayuka da dama a Nijar, ciki har da yankunan hamada.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa sauyin yanayi na taka rawa a ambaliyar ruwa da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ke shafar kasar a shekarun baya-bayan nan. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Nijar ta ce a bara mutane 52 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa, hakazalika bala'in ya kuma shafi wasu 176,000.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan jihar Jigawa
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan jihar Jigawa

A lokacin rani dai al'ummar Nijar na fama da matsalar fari da tsananin zafi.

Ya zuwa yanzu, yankin Maradi ne ya fi fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, inda 14 daga cikin mace-mace 21 da aka samu daga jihar ne, a cewar Bako a lokacin da ya yi sanarwar ta talabijin.

Har yanzu dai gwamnatin kasar ba ta bayyana wani shiri na tsugunnar da mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG