KUMASI, GHANA - Hakan ne ya janyo tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu, sannan Gwamnatin Ghana ta tura tawaga ta musamman tare da tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin kasar ta Burkina Faso.
Wani matakin da gwamnatin Ghana ta ce zai ci gaba da karfafa zumunci tsakanin kasashe biyun musamman a kokarin da ake yi na neman kawar da aika-aikar ‘yan ta'adda a Afirka ta Yamma.
Tawagar da suka gana da gwamantin sojin Burkina Faso ta kunshi Ministan Tsaron kasar Albert Kan Dapaah da wasu manyan jami’ai a ofishin Ministan Harkokin Wajen Ghana.
Ministan tsaron kasar Albert Kan Dapaah ya fada wa manema labaru bayan ganawarsu da gwamnatin soji karkashin jagorancin Ibrahim Traore cewa "mun tattauna kan yadda za mu karfafa zumunci tsakaninmu tare da samun fahimtar juna game da ganawar da Ghana tayi da Amurka mai alaka da hada kai domin samar da dawwamammen zaman lafiya a yankinmu."
Ministan ya kara da cewa "mun kuma tattauna kan taimakon da Ghana da ECOWAS za ta ringa bai wa Burkina Faso karkashin shirin Accra Initiative dake kokarin kawar da ta'addanci a yankinmu.”
Mai magana da yawun gwamnatin Ghana ta fannin tsaro tare da tsare- tsaren gwamnati Palgrave Boakye Danquah ya ce "a yanzu komai ya lafa tunda Ministan Tsaron Kasar ya wakilici shugaban kasa wajen ganawa da gwamnatin Burkina Faso kuma mun amince kan hada kai domin yaki da ta'addanci a yankin.”
Umar Sanda Ahmad tsohon jami’in diflomasiyya kana mai sharhi kan harkar tsaro ya ce matakin da gwamnatin Ghana ta dauka din yayi daidai.
An samu tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu ne biyo bayan ikirarin da Shugaban Ghana, Nana Addo, ya yi cewa gwamnatin soji ta Burkina Faso ta dau hayar sojojin Wagner na Rasha domin kawar da ta'addanci a kasar, abinda ke barazana ga tsaron Ghana, inda Ghana tayi Allah wadai da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
Abinda ya kai Burkina ga janye jakadanta daga Ghana tare da gurfanar da jakadan na Ghana a Burkina Fason.
Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5