Shugabannin sun fadi hakan ne a wajen taron da gidauniyar hadin kan Hausawan Duniya, reshen Ghana, ta shirya, domin karrama wasu shugabannin Hausawa da suka taka rawar gani wajen ci gaban Hausawan Ghana da kuma rantsar da sabbin shugabannin kungiyar, da aka gudanar Accra.
Gidauniyar Hadin Kan Hausa da Hausawan Duniya, kungiya ce da aka kafa ta, musamman, domin hadin kan Hausawa da masu magana da harshen Hausa. Kungiyar ta gudanar da taron karramma wasu shugabanni da Sarakunan gargajiya da suka yi fice wajen daga martaban Hausa da Hausawan Ghana.
Daga cikin wadanda aka karrama akwai Sarki Kabiru Kadiri English, sarkin Hausawan yankin Greater Accra; da Sarkin Zango, sarki Yahya Hamisu Bako; da kuma Sarki Lamido Mohammed Jibril Sissy, sarkin zangon Anya. Dukkansu an karrama su da digiri digirgir (Honorary Doctorate Degree).
Wasu daga cikin shugabannin da aka nada sun hada da Limamin limamai na Ghana, Sheikh Dokta Usman Nuhu Sharubutu, wanda aka nada a matsayin Garkuwan wannan kungiya, da Dokta Sharif Mohammed, shugaban kungiyar reshen Ghana.
Shugaban kungiyar Hadin kan Hausa da Hausawa na duniya, Kwamanda Alhaji Mohammad Saeed, a jawabinsa ya bayyana cewa, sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Daura da Alhaji Aminu Dantata duka sun ba da goyon baya ga wannan kungiyar.
Shugabannin Hausawa, Sarkin Zango, Yahya Hamisu Bako da Sarki Lamido Jibril Sissy da kuma sabuwar mai Hulda da jama’a na kungiyar, Hajiya Hafsat Kadiri English sun jaddada kira ga samun hadin kai tsakanin Hausawan Ghana.
Kodinetan shugaban kasa na asusun ci gaban zango, Alhaji Ben Abdallah Banda ya taya wadanda aka karrama murna, a madadin mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia.
Saurari rahoton Idris Abdulla Bako cikin sauti: