Bayan shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya jagoranci rantsuwar mubayi’a, shari’a ,da kuma na sirri ga alkalai 15, wadanda suka kunshi maza 10 da mata 5, da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Accra, shugaban kasar ya yi kira ga alkalan kotun daukaka karan da su tunkari duk wasu kararrakin da suka zo gabansu da gaskiya da inganci. Yace, yana da matukar muhimmanci a sami alkalai masu gaskiya da cikakkiyar masaniyar doka. Halin da alkalai ke yanke hukunci kan hukuncin da kananan kotuna suka yanke, tare da bayyana su a matsayin doka abu ne da ba za a amince da shi ba.
Mai shari’a Afia Serwah Asare-Botwe, ta yi jawabi a madadin sauran takwarorinta 14. Tace, “Za mu tabbatar da ratsuwar shari’a da muka yi cikin himma, da aminci, da ladabi da gaskiya, kuma za mu yi adalci ba tare da tsoro ko son rai, ko soyayya ko mugun nufi ba”.
Kotun daukaka kara ita ce babbar kotu ta biyu a cikin jerin manyan kotunan Ghana. Kuma a halin yanzu tana da alkalai 34 a fadin kasar, yanzu karin 15 din nan da shugaban kasa ya yi, ya kawo adadinsu zuwa 49 gaba daya.
Wannan karin alkalan da shugaban kasa ya yi, kamar yadda, Lauya Hummu Zakari, na ofishin Antoni Janar ta nuna, zai yi tasiri wajen rage kalubalen da sashen shari’a ke fuskanta, musamman ta bangaren jinkirin yanke hukunci da ake samu a kotunan daukaka kara sabili da karancin alkalai.
Mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Salahuddeen Yunus Wakpenjo, ya shawarci sabbin alkalan da su nuna kwarewa da suka samu a kotunan baya da aminci wajen gudanar da aikinsu.
Kundin tsarin mulkin Ghana ne ya baiwa Shugaban kasa alhakin nada alkalan kotun daukaka kara, da na babbar kotu, da shugabannin kotunan yanki, amma bisa ga shawarar majalisar shari'a ta kasa.
Saurari rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti: