ACCRA, GHANA - Hakan ya bayyana a fili saboda zaman lafiya da kwanciyar hankali da kasar Ghana ke gani a duk lokacin bukukuwan manyan addinai guda biyu kamar bikin Kirsimeti da na Idi babba ko karama, Musulmai da Kirista suna haduwa domin yin bukukkuwar tare.
Babban abin da ya fi daukan hankali kuma shi ne kasancewa Musulmi ba sa cin yankan wadanda ba Musulmi ba kamar yadda addini ya bayyana, wasu Kiristocin a Ghana suna gayyatar Musulmai da su yi musu yankan dabbobin su a lokacin bukukuwar Kirsitmeti saboda idan sun ba su abincin za su iya ci.
Kwaku dan cocin Presbyterian Ghana ya ce suna gayyatan Musulmai a ranar 31st ga watan Disamba wato 31st night ko wace shekara kuma Musulmi ke musu yanka.
Pasta Fillix na cocin Author of Fire a birnin Accra ya ce, Kiristocin Ghana da Musulmi na zaman lafiya, kuma akwai fahimtar juna babu tashin hankali tsakaninsu.
Mallam Rabiu Maude dan Masanin birnin Accra ya ce yana da kyau sauran kasashe musamman kasashen Afirka su yi koyi da Ghana.
Mafi girman addini da yawan mabiya a Ghana shi ne addinin Kirista wadanda ke da kaso 71.2 %.
Saurari cikakken rahoto daga Hawawu AbduKarim: