Haka kuma mutanen da ECOWAS take da aniyar karewa, a karshe za su kasance masu gudun hijira a wasu kasashen, tare da karawa kasashen yankin Afirka ta Yamma matsalar tattalin arziki da take fuskanta da ma wasu munanan sakamako.
Sun bayyana hakan ne a taron manema labarai da ofishin limamamin limaman Ghana ya shirya domin bayyana matsayar Musulman Ghana kan dambarwar Nijar.
Dakta Shaikh Usman Nuhu Sharubutu, ya bayyana dalilin taron kuma ya mika godiya ga Allah (SW) da ya sa ba zubar da jini a kasar Nijar ba, sannan kuma ya yi kira ga wadanda lamarin ke hannunsu da a yi gyara cikin lumana.
Taron ya samu halartar shugabannin kungiyoyin darikar Tijjaniya, Shi’a, Ahlul Sunnan wal Jama’a, da Ahmadiya. Shugaban Ahmadiya, Maulvi Mohammed Bin Salih ne ya karanta jawabin ga manema labarai, a madadin shugabannin. Suka ce,
“A matsayinmu na shugabannin al'ummar Musulmai a Ghana, mun damu matuka game da halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar”.
Kuma sun yi Allah wadai da juyin mulki baki daya, amma a yi dalci kamar yadda Kur’ani ya ce wajen yanke hukuncin matakin da za a dauka. Shugabannin Musulmi a Ghana sun kuma yi kira da a yi la’akari da bukatun mutanen Nijar tare da kiyaye tsaronsu. Sun kuma jaddada matsayarsu na kada a dauki matakin soji domin yaki a Nijar zai kara ta’azzara batun ta’addancin da ya addabi yankin; suka ce maimakon haka a ci gaba da diflomasiya.
“Muna kira ga shugabannin yankin da wasu cewa, duk wani hukunci da za su dauka kan juyin mulki a Nijar, tilas ne a fifita tattauna”.
A gefen taron, Zaeem Tijjaniya na Ghana, Shaikh AbdulWadud Harun Cissey ya ce:
“Sun hadu ne domin su baiwa ‘yan Nijar da Afirka hakuri domin dukkansu daya ne; Najeriya da Nijar daya ne; Nijar da Ghana daya ne; dukkanmu daya ne. Abinda ya taba daya, ya taba mu duka ne”. Domin haka suna kira da a yi sulhu ba da makami ba.
Limamin kungiyar Shi’a na Ghana, Shaikh Abubakar Kamaludeen ya ce duk da cewa ba su goyi bayan juyin mulkin, amma kuma ya kamata shugabanni su gyara halayensu, su bar zalunci da cin hanci da rashawa, kuma su gyara tattalin arzikin kasa yadda al’umma za su samu kwarin gwuiwa a kan su.
A karshe shugabannin sun nuna cewa idan diflomasiyyar siyasa ba ta yi nasara wajen shawo kan lamarin ba, a koma ga diflomasiyyar addini, za a yi nasara.
Saurari rahoton Idris Abdullah:
Your browser doesn’t support HTML5