Ana kyautata zaton shahararren dan kwallon nan na Liberia George Weah, wanda ke jam'iyyar adawa ta CDC, zai yi na'am da bukatar magoya bayansa cewa ya shiga takarar zaben Shugabnan kasa na shekara ta 2017.
WASHINGTON, DC —
Weah, wanda ya zama Sanata mai wakiltar Karamar Hukumar Montserrato a karon farko, ya fara shiga takarar Shugaban kasa ne a 2005 lokacin da ya zama na biyu bayan Shugaba Ellen Johnson Sirleaf. Ya saka shiga takara a 2011, a matsayin Mataimakin Shugaban kasa ga Winston Tubman kuma wannan karon ma ta biyu jam'iyyrsu ta zama bayan ta su Sirleaf.
Nathanial McGill, Shugaban Jam'iyyar ta CDC ya ce gwamnatin Shugaba Sirleaf ta tsawon shekaru 10 ta gaza kyautata rayuwar 'yan Liberiya duk kuwa da goyon bayan da ta samu na kasa da kasa.