Ana sa ran shugaban da ya fi kowane shugaba dadewa yana mulki a Afirka, watau shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang shine zai lashe zaben kasar don sake yin wani wa’adin shugabanci. Yanzu haka mutanen kasart na jiran jin sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadin da ta gabata.
Har yanzu kwanaki 3 bayan zaben, manyan hotunan yakin neman zabe na shugaba Theodoro Obiang Nguema Mbasogo na nan manne a jiki gine-gine da ke birnin Bata
Bisa doka, kamata yayi a kawarda duk wasu kayayyakin yakin neman zabe kwana daya kafin zabe.
Iyalan Obiang sun shugabanci kasar tun daga lokacin da ta sami ‘yancin kanta a shekarar aluf dari tara da sittin da takwas. Shugaban kasar na yanzu ya dare kan karagar ne bayanda ya hambare gwamnatin kawunsa a juyin mulkin da aka yi a shekarar aluf dari tara da saba’in da tara.
Equatorial Guinea na daya daga cikin manyan kasashen kudu da hamada da ke sarrfa mai da iskar gas. Hakan da kuma kasancewar ‘yan kasar basu da yawa na nufin kasar na da kudaden da ake kashewa na cikin gida mafi yawa a Afrika, a cewar adadin rahoton Majalisar dinkin duniya, na shekarar 2014, amma kuma ita ce ka sa ta kasaa Jerian kasashen dake cigaba.
Iyalin Obiang na daya daga cikin wadanda Amurka da Turai ke gudanar da bincike akansu game da badakalar miliyoyin kudade.
Shugaban ya sami nasarar zabuka har saiu biyar, bai taba samu nkasa da kashi 95 na kuri’u ba. Sai dai jam’iyyar hamayya ta CPDS ba ta yi zaben ba, tana mai cewahukumar zaben kasar na nuna son kai.