Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar girka sojoji a yammacin Sahara


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya shirya kada kuri’a ranar Juma’a mai zuwa game da bukatar Amurka na farfado da ajiye dakarun kiyaye zaman lafiya a Yammacin Sahara, bayan Morocco ta kori ma’aikatan MDD 83 a watan da ya wuce.

Wa’adin shirin wanzar da zaman lafiyar da ake ciki a yankin yammacin Saharar ya kare a ranar Asabar din data wuce, sannan Babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya gargadi yiwuwar barkewar yaki idan ba a sabunta shirin wanzar da zaman lafiyar ba.

Ya fadawa kwamitin sulhun cewa, akwai yiwuwar ‘yan ta’adda da masu tsatstsauranj ra’ayi sun yi amfani da damar wajen dagula al’amura.

Haka zalika yarjejeniyar tsagaita wuta na iya tabarbarewa ta haifar da rikici, in har aka tursasa fitar dakarun kiyaye zaman lafiyar da ake wa lakabi da MINURSO.

Ko kuma in har aka ce sun sami kansu a halin da zai zama ba za su iya aiwatar da nauyin da kwamitin ya rataya a wuyansu na wanzar da zaman lafiyar ba.

Shirin wanzar da zaman lafiyar ya fara ne a shekarar 1991. Domin sa ido bisa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Morocco da ‘yan yakin sa kai na ‘yan tawayen Polisario Front da kasar Aljeriya ke marawa baya.

XS
SM
MD
LG