Gasar Kofin Duniya Ta Mata: Tinubu Ya Mika Sakon Fatan Alheri Ga Tawagar Super Falcons

'Yan wasan Super Falcons (Facebook/NFF)

Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya mika sakon fatan alheri ga 'yan wasan kwallon Najeriya na Super Falcons yayin da suke shirye-shiryen karawa da Australia a wasansu na biyu na rukuni a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a Australia da New Zealand 2023.

WASHINGTON, D.C. -

“Kamar sauran 'yan Najeriya masoya kwallon kafa, Shugaba Tinubu, yamai alfahari da rawar da ‘yan Super Falcons suka taka a wasan farko da kasar Canada, babbar abokiyar hamayyarta kuma mai rike da kofin gasar Olympics.” Kakain Tinubu Dele Alake ya ce cikin wata sanarwa.

Kungiyar Super Falcons ta Najeriya

Cikin sanarwar, Tinubu ya yi amannar cewa wasan da za a yi a ranar Alhamis zai kasance wasa mai ban sha'awa wanda zai kai ga nasara ga 'yan wasan na Najeriya.

A ranar Alhamis Najeriya za ta kara da Australia mai masaukin baki.

Yayin da yake amincewa da gagarumin nasarorin da Super Falcons ta samu a matsayinta na babbar kungiyar kwallon kafa ta mata a Afirka, Shugaba Tinubu yana da kwarin gwiwar cewa hada sabbin kwararru da jiga-jigan zai kara kaimi ga nasarar Najeriya a harkar kwallon kafa ta mata har zuwa wani matsayi mai girma a wannan gasa.

Super Falcons

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan wasan da masu horar da ‘yan wasan kasar goyon bayan duk wani ‘dan Najeriya, inda ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da nuna kwazo, da kwazon Najeriya a ciki da wajen filin wasa, tare da zama jakadun kasar da suka cancanta.