WASANNI A TAKAICE * A kwallon kafa na Matan Afurka, Morocco ta buge Najeriya *'Yar gudun nan ta Nijer, Amina Seyni, ta sake burgewa
Birnin Nkonni, Niger —
Zamu soma labarun wasaninmu na yau da jamhuriyar Nijer, inda a salamainin daren jiya ne, zuwa karfe 2 na dare agongon Nijer da Najeria, yar jamhuriyar Nijer din nan, Amina Seyni, mai gaggawar gudun nan, da ke rike da kamben tseren mita 200 na Africa da ma ta 2 a Nahiyar a tseren mita 100, ta yi wa takwarorinta na duniya a turmi na neman shiga tseren kusa da na karshe na mita 200 na duniya shashau a EUGENE a kasar America.
A yau din ma, a irin wannan lokacin ne, Amina Seyni zata yi kokarin kai ga tseren na duniya na karshe na mita 200.
A halartarta a tseren mita 100, ta tsaya a tseren kusa da na karshe, yayin da mai horar da ita, ya ce wannan layin na mita 100 sabo ne a gare ta, duk da yake a nan gaba, zata yiwa masu wannan gudun mata na 100 a duniya, amma a cewar kocin nata, a wannan ajin mita 200, akwai zaton ta yi shamata a wadannan wasanin na tsere na duniya.
+++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++
Duk dai a jamhuriya ta Nijer, kungiyar kwallon kafa ce ta AS DOUANES TA custum ta lashe kofin kwallon kafa na kasar na wannan shekara ta 2022 a Stade General Seyni Kountche a bainar shugaban kasar ta Nijer Bazum Mohamed da Mataimakin shugaban majalisar dokoki ta kasa da membobin gwamnatin kasar da yan kallo sama da dubu 27 gaban USGN.
Kungiyoyin 2 sun share mintoci 90 suna kai wa juna hari, inda a mintoci na 40 ne, mai lamba 34 Boubacar Soumana Hainikoye mai lakanin suna Déko na kungiyar USGN ya kai kwallo raga.
Amma a mintuna na 73 ne AS Douanes ta Custums, ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida da Issa Mossi Issa dake buga wa kungiyar Kwallon kafa ta jamhuriyar Nijer Mena National.
Alkalin wassanin kwallon kafa dake karkashin FIFA Mohamed Ali ne ya jagoranci wannan wasan.
Haka a ka cigaba har mintuna 90, daga nan sai bugun daga kai sai tsaron gida, inda AS DOUANES ta Custums ta yi nasara da ci 4 - 3 gaban USGN, inda ta lashe kofi da shugaban kasar Nijer da kan sa ya mika musu da tsabar kudi miliyon 20 na SEFA yayin da USGN ta samu Miliyon 5 na sefa.
Hasali ma, AS NIGELEC ta wutar lantarki da ta lashe teburin kwallon kafa ta Nijer ta super ligue 2022, ta samu tsabar kudi sefa miliyon 20, yayin da AS DOUANES da ta zo ta 2 a teburin super ligue na rukuni na farko na jamhuriyar Nijer ta samu kudi miliyon 5.
Gabanin soma wasan ta karshe ta kofin kwallon kafa ta Nijer tsakanin AS DOUANES da USGN, an yi karawa ta karshe ta wasanin kwallon kafa ta yan makaranatar Faramare ta Nijer yan kasa da shekaru 13, inda yan wasan Diffa su ka lashe na Yamai a cin daga kai sai mai tsaron gida.
---------------------------------------------------------------------------------------
A wasanin kofin Nahiyar Afurka na kwallon kafa na mata kuwa, kasar Morocco mai masaukin baki da gwabcikewa kasar Najeriya dake rike da wannan kamben da ci 4 - 3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a jiya, bayan kungiyoyin sun share mintoci 120 da ci 1 - 1.
'Yan Najeriya sun kammala wasan su 9 daga cikin 11 da suka soma karawar, wannan ko bayan jan kati guda 2, Halimatu Ayinde, Mai bugawa a tsakiya wa club din FK Minsk a kasar Biélorussie, da a ka kora saboda mugun wasa a minti na 48 sai Rasheedat Ajibade, Mai cin kwallaye ta Atlético de Madrid da a ka kora minti na 71 saboda mugun wasa.'
Super Falcons din sun fice a wasan kusa da na karshe, alhali har sau 3 biye da juna a baya - bayan nan suna lashe kofin.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mammane Bako:
Kofin Duniya ta Qatar 2022
Nuwamba 01, 2022