Sheikh Gumi, ya shahara wajen shiga dazuka wajen Fulani ‘yan bindiga domin sauraronsu tare da fadakar da su game da tayar da kayar bayan da ke faruwa tsakaninsu da al’umma.
A daidai lokacin da ake muhawara kan hanyar da ya Kamata abi domin samar da zaman lafiya, wasu na ganin shiga dazuka tare da kame ko kashe Fulanin shi ne mafita ga matsalar tsaro a arewacin kasar, wasu kuma musamman irin su Sheikh Gumi, na ganin samar da sulhu da Fulanin shi ne abin da ya kamata hukumomi su yi.
Kasancewar su ma ‘yan Najeriya ne, kuma sun dauki makamai tare da fadawa tarkon aikata laifuka ne, biyo bayan rashin ba su kulawa tare da kashe ‘yan uwansu da dabbobinsu da aka yi a baya.
Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya zanta da Sheikh Ahmed Gumi, game da ayyukan da ya ke gudanarwa don samar da zaman lafiya tsakanin al’umomi da Fulani ‘yan bindiga.
Sheikh Gumi, ya ce ba ya jin tsoron shiga dazukan da Fulani suke, idan ma akwai abin da ya ke tsoro shi ne sojoji su yi musu ruwan bama-bamai a lokacin da suke cikin dajin, duk da ya ce a duk lokacin da za su shiga irin wannan aiki, suna sanar da hukumomin tsaro.
Saurari cikakkiyar hirar Isah Lawal Ikara da Sheikh Ahmed Gumi.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Sheikh Ahmed Gumi, Fulani, Nigeria, da Najeriya.