Babbar sakatariyar hulda da ‘yan jarida ta gwamnan jihar Naija Mary Berje, a wata sanarwa ta ce an sako mutanen ne a daren jiya wayewar garin yau Litinin.
Sun hada da mutane 39 ragowar mutane 47 da ke cikin motar kamfanin sufuri na jihar, wadanda aka dauke su kafin daliban Kagara. Da ma can an sako mutane 8 daga cikinsu.
An hannunta mutanen da aka saki ne ga jami’an gwamnatin jihar, a wani wuri da ba’a bayyana ba a cikin jihar Zamfara.
Jaridar THISDAY ta Najeriya ta ruwaito Sakataren Gwamnatin jihar ta Naija Alhaji Ahmed Matane, yana cewa masu garkuwa da daliban ba su nemi kudin fansa ba, to amma ana nan ana tattaunawa da su domin sako daliban.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwamnatin jihar sun isa garin Kagara tun a daren Lahadi, suna jiran sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Sakin mutanen 53, ya haifar da kwarin gwiwa da sa ran cewa za’a sako daliban da malamansu a yau Litinin.
Wasu rahotanni kuma na bayyana cewa sakin mutanen, da kuma kokarin ganin an sako daliban Kagara, duk sun gudana ne ta hanyar sulhu a karkashin jagorancin malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gummi.