Rikicin satar mutane don neman kudin fansa da ake cigaba da fuskanta a Arewacin Najeriya, ya kai duk inda ake kaiwa, kamar yadda jama'a ke cigaba da kokawa. Akan dora laifin ga Fulani makiyaya, inda su kuma ke dora laifin akan gwamnati.
Akasarin mayakan nan da ke kama mutane don neman kudin fansa, suna yin hakan ne a bisa dalilin rashin adalci da ake yi musu, kamar yadda wasu daga cikin masu garkuwa suka bayyana wa Muryar Amurka.
A duk lokacin da aka yi alkawali da mahukunta, su kan saba akan hakan, sau da yawa akan kashe musu 'yan uwa ko mai da su saniyar ware, babu wani abu da suka samu daga hannun gwamnati, wanda hakan yasa suka shiga cikin wannan aikin.
A duk lokacin da aka samu fahimta tsakanin mahukunta da masu garkuwa, sai a bar su cikin daji tare da makamai, amma ba a kokarin ganin an kyautata musu, don haka suka ga cewar abu da ya fi dacewa shi ne, su shiga daukar matakin kwatar ma kansu hakkinsu.
Gwamnati ta sare daji, babu wani abun more rayuwa da bafullatani zai ce ya mora a kasar, saboda irin matakai na koma baya da ake saka Fulani a ciki. Basu da wani dalilin daukar matakan da suke akai yanzu sai don rashin adalci da ake yi musu.
Ana iya sauraron rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi cikin sauti.