Matar mai suna Aisha ta ce bayan ta kammala ziyarta da zumman washegari zata dawo kano- cikin dare da misalin karfe 11 na dare sai karar harbe-harben bindogi ya tashe su daga barci da rashin sanin ashe gidan da take iftila’n Zai afkawa.
Ta bayyana cewa a cikin duhun suka ji ana hayya hayya sai suka ga maza kimanin su ashiri kowanne dauke da bindiga suka zo su ka tasa keyarsu zuwa cikin daji suka yi ta tafiya basu kai Inda suka ajiye su ba har sai washegari da misalin karfe 6 na safiya.
Aisha ta ce,kafin su isa inda aka ajiye su, sai da suka tsaya a wani gari maharan suka hada da wasu mutane kimanin goma sha daya da maharan suka kama a kauyen. Bisa ga cewar ta da suka isa kauyen da aka yi garkuwa da su,sai suka iske wasu mutane da dama kimanin 100 a iya ganinta da kungiyar ta yi garkuwa da su kafin kama wadanda ta tawo da su tare da ita.
Abinda ‘yan garkuwan ke bukata
'Yan garkuwan dai sun bukaci su goma sha dayan da aka kama kowannen mutum ya bada naira dubu dari biyar, wato miliyan biyar da dubu dari biyar a kan su duka.
Bayan an tuntubi’yan uwan kowa ta wayar salula sai aka yi yarjejeniyar biyan dubu dari biyu da hamsin akan kowanne mutum aka yi sa’ar aika musu da miliyan daya da dubu dari biyar.
Ta ce gari ne Inda aka ajiye su amma ta ce masu garkuwan sun kori 'yan garin suna ajiye wadanda suka kama, yayinda su ke sa wasu daga cikinsu suka rika yi musu girki.
Aisha ta ce a dajin da aka ajiye su kungiya kungiya ne har kashi biyar. Bisa ga cewarta akwai kungiyar Yellow, da kungiyar Kachalla sai na Bugari sai kungiyar Basullube da kuma wata kungiyar wani ta biyar.
Ko an ci zarafinsu?
Aisha ta sami kanta a kungiyar Yellow wanda ya ce baya garkuwa da mata akasi ne ya sa aka kama su. 'Yan kungiyarsa basa fyade basa musgunawa mata sai dai maza daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su wasu maza sun sha bugu.
Daga karshe dai Aisha ta ce ta samu nasarar kubuta ne sakamakon rashin lafiyar da tayi fama da shi bayan shafe kwanaki goma sha daya da tayi,
Bisa ga cewar Asiha, 'yan kungiyar Yellow sun shaida mata cewa bada son ransu suke wannan aiki ba, kuma suna bukatar gwamnati ta zauna da su .
Saurari cikakken bayanin Aisha a hirar su da Baraka Bashir: