Ana sa ran yanayi ya cigaba da tabarbarewa tsawon yinin yau Laraba sakamakon yadda kadawar guguwa da basassheyar iska ke kara rura wuta a unguwannin Palisade na yankin Pacific da kuma akalla wasu unguwannin 2 dake Los Angeles, kamar yadda masu hasashen yanayi suka bayyana.
Gwamnan California Gavin Newsom ya ayyana dokar ta baci a fadin jihar a jiya Talata.
Gine-gine da dama sun lallace haka kuma kusan eka dubu 3 ta kone a Palisade ta yankin Pacific, wacce ke tsakanin garuruwan Santa Monica da Malibu dake bakin tekun, a cewar jami'ai. Yankin ya kasance mazaunin jaruman fina-finai da mawaka.
Hanyoyi sun cunkushe da mutanen dake kokarin tserewa gobarar, wasu sun kyale motocinsu yayin da harshen wuta ke lasarsu sannan hayaki da tartsatsin wuta sun turnuke sararin samaniyar Los Angeles da kewaye cikin dare.
Jarumi Steve Guttenberg ya shaidawa tashar talabijin ta Ktla cewar motocin da wasu suka kyale akan hanya sun hana wasu abokansa tserewa.
"Yana da matukar mahimmanci kowa ya kasance tare da juna sannan kada a damu da dukiya. Kawai a fice daga yankin, inji guttenberg." Kawai ka tattara makusantanka ka fice
-AP