Jami’an gwamnati a jihar California nan Amurka sunce ala tilas dubban mutane suka fice daga gidajensu a yayinda gobarar daji ta lalata wani yanki a arewacin jihar da yake farfadowa daga gobarar dajin da suka auku cikin ‘yan shekarun da suka shige.
Hukumomi sunce wutar dake ci ba kakautawa tuni ta lalata hecta ashirin da biyu na fili kusa da dajin Mendocina, kimamin kilomita dari da goma a arewa maso yammacin Sacramento baban birnin jihar.
Gobarar ta tilastawa fiye da mutane dubu uku barin gidajensa harma gwamnan jihar Jerry Brown ya ayyana dokar ta baci a karamar hukumar Lake.
Jami’an kashe gobara sunce yan kwana kwana maitan da talatin ne suka aikin kashe gobarar a karamar hukumar Lake da tuni ta lalata fiye da hecta dubu uku da dari uku na.
A jiya litinin dai ‘yan kwana kwana sun yi amfani da jiragen sama masu saukar angulu da suke zubar da ruwa da kuma manyan motoci buldoza, to amma har yanzu suna fafitukar ganin sun kashe gobarar.
Facebook Forum