A California shugaban kasa, ya yi watsi da batun da ake yi na canjin yanayi ne ke janyo yawan tashin wuta mai tsanani, inda ya nanata kiran da yake yi ga yankin yammacin Amurka da su canza salon kula da gandun dajin su.
Idan bishiyoyi suka fadi, a cikin dan lokaci suna bushewa suna zamewa ne tamkar kiraruwa, inji Trump yayin da ya isa California. Kuma zasu iya tada gobara. Haka ma ganye, idan suka bushe a kasa tamkar makamashi ne.
Biden yana fada a jihar sa ta Delaware cewa, Kin amincewa da batun canjin yanayi da Trump ya yi ba shine ya tada gobarar ba, Amma idan shugaban ya samu wa’adi na biyu, za a ga irin wannan mummunar gobara da dama mai yawan barna da muni
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yanda Trump ke tinkarar lamarin, yana watsi da batutuwan gaskiya kana yana karyata abin dake faruwa, abin da ya kira sallamawa tasirin canjin yanayi.
Dubun dubatar mutane ne suka kauracewa gidajen su.
Facebook Forum