A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a ranar Litinin, shugabannin sun amince da sabon yunkurin da kasashen Amurka, Qatar da Masar suka yi na kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas da aka kwashe watanni 10 ana yi.
Masu shiga tsakani sun shafe watanni suna kokarin ganin bangarorin su amince da wani shiri mai matakai uku wanda Hamas za ta saki sauran mutanen da aka kama a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba domin musanya wa Falasdinawa da Isra'ila ke daure a gidan yari sannan Isra'ila za ta janye daga Gaza.
"Dole ne a kawo karshen fada a yanzu, kuma dole ne a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su da Hamas ke tsare da su. Al'ummar Gaza na bukatar kayayyakin agaji cikin gaggawa ba tare da wata tangarda ba,." In ji sanarwar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da firaministan Birtaniya Keir Starmer ne suka sanya wa sanarwar hannu.
Sanarwar ta kuma yi kira ga Iran da kawayenta da su kaurace wa duk wani harin ramuwar gayya da zai kara ruruta wutar rikicin yankin bayan kashe wasu manyan mayakan shugabannin biyu a watan jiya a Beirut da Tehran.
-AP