Norway, Spain da Ireland a ranar Talata sun zama kasashe na baya-bayan nan da suka amince da kafa kasar Falasdinu a hukumance.
Kasashen uku sun ce sun yi kokarin kara kaimi wajen ganin an tsagaita bude wuta a yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza.
Kasashen uku sun ce suna fatan matakin da suka dauka zai sa sauran kasashen Tarayyar Turai su bi sawu.
"Wannan ce hanya daya tilo na ci gaba zuwa ga abin da kowa ya amince da shi a matsayin mafita daya tilo don cimma makomar zaman lafiya, da zai ba kasar Falasdinu damar rayuwa kafada da kafada da kasar Isra'ila cikin zaman lafiya da tsaro," in ji Firai Ministan Spain Pedro Sanchez yayin wani jawabin da yayi a talabijin.
Spain ta amince da kafa kasar Falasdinu da suka hada da zirin Gaza da gabar yamma da gabar kogin Jordan karkashin hukumar Palasdinawa da gabashin Kudus a matsayin babban birnin kasar.
Matakin nasu wanda ya harzuka Isra'ila ya kai kasashe 145 daga cikin kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya da suka amince da kasar Falasdinu.
Kasashen sun haɗa da yawancin Gabas ta Tsakiya, Afirka da ƙasashen Asiya, amma ba Amurka, da Kanada, da yawancin kasashen yammacin Turai, Australiya, Japan ko Koriya ta Kudu a ciki.
A watan Afrilu, Amurka ta yi amfani da kujerar naki a yayin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don hana yunkurin Falasdinawa na zama cikakkiyar kasa mamba ta Majalisar Dinkin Duniya.
Dandalin Mu Tattauna